Markus
1
Wannan itace farkon bisharar Yesu Almasihu, Dan Allah. kamar yadda aka rubuta cikin littafin annabi Ishaya. Duba, ina aika manzona, a gabanka, wanda zai shirya maka hanya. Akwai murya mai kira a jeji, tana cewa ka shirya hanyar Ubangiji. ka daidaita ta. Yahaya ya zo, yana baptisma acikin jeji yana wa'azin tuba, domin gafarar zunubai. Dukan kasar Yahudiya da mutanen Urshalima suka zo wurin sa, a ka kuma yi masu baptisma a kogin urdun. suna furta zunubansu. Yahaya yana saye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma da damara ta fata a kugunsa, abincinsa fara ce da zuma. Yana wa'azi, ya ce “akwai mai zuwa a bayana wanda ya ke da iko fiye da ni. wanda ko maballin takalminsa ban isa in kwance ba. Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki''. Sai ya kasance a kwanakin nan Yesu ya zo daga Nazarat ta Galili, sai Yahaya ya yi masa baptisma a kogin urdun. 10 Sa'adda Yesu ya fito daga ruwan, sai sama ta bude, sai Ruhu ya sauko a bisansa da kamanin kurciya. 11 Sai wata murya ta zo daga sama, tana cewa, “Kai kaunataccen Dana ne. zuciyata ta na murna da kai kwarai''. 12 Sai Ruhu ya iza shi zuwa jeji. 13 Yana a jeji kwana arba'in, Shaidan yana jarabtar sa. Yana cikin jeji da dabobi, sai malaiku su ka yi masa hidima. 14 Bayan da aka kama Yahaya, Yesu ya shiga kasar Galili yana wa'azin bisharar Allah. 15 Yana cewa, “Lokaci ya yi, gama mulkin Allah ya kusato. Ku tuba ku bada gaskiya ga bishara”. 16 Sa'adda ya ke wucewa a gefen takun Galili, sai ya ga Saminu da Andarawus, dan'uwansa suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. 17 Yesu ya ce masu ku zo, ku biyo ni, ni kuwa sai in maisheku masuntan mutane”. 18 Nan da nan suka bar tarun su, suka bi shi. 19 Sa'adda Yesu ya yi tafiya kadan, sai ya ga Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan'uwansa; suna gyaran tarunsu a jirgin ruwa. 20 Sai ya kira su, su kuwa suka bar mahaifinsu Zabadi a jirgin ruwan da ma'aikatansu, sai su ka bi shi. 21 Da su ka shigo cikin kafanahum, a ranar asabar, Yesu ya shiga majami'a ya koya masu. 22 Su ka yi mamakin koyarwarsa, domin ya na koya masu da iko ba kamar marubuta ba. 23 A nan cikin majami'a akwai wani mutum mai kazamin ruhu, sai ya yi ihu da karfi. 24 Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah”. 25 Sai Yesu ya tsauta wa kazamin ruhun ya ce, “Ka yi shiru ka fita daga cikinsa”. 26 Bayan da kazamin ruhun ya buga shi kasa, sai kazamin ruhun ya yi ihu sa'annan ya fita daga jikinsa. 27 Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!” 28 Nan da nan labarinsa ya bazu ko'ina a dukkan kewayen kasar Galili. 29 Bayan da suka bar majami'a, sai su ka shiga gidan Saminu da Andarawus, suna kuma tare da Yakubu da Yahaya. 30 Surikar Saminu tana kwance ba lafiya tana fama da zazzabi. Sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31 Sai ya zo, ya kama hannunta, ya daga ta, sai zazzabin ya sake ta, ta fara yi masu hidima. 32 Da yamman nan, bayan da rana ta fadi, sai su ka kawo masa dukan marasa lafiya da masu fama da aljanu. 33 Dukan mutanen garin su ka taru a bakin kofa. 34 ya warkar da masu ciwo da yawa da masu chututtuka iri-iri, ya kuma fitar da bakaken aljanu, amma bai yarda aljanun su yi magana ba domin sun san shi. 35 Ya tashi da sassafe, tun da sauran dare, ya tafi wurin da ba kowa, a can ya yi add'ua. 36 Saminu da wandanda suke tare da shi suka neme shi. 37 Suka sa me shi, sai su ka ce masa, “kowa yana nemanka”. 38 Ya ce, bari mu tafi wani wuri, zuwa wadansu garuruwan da ke kewaye, Saboda in yi wa'azi a can kuma. Wannan shi yasa na zo nan''. 39 Ya tafi dukan kasar Galili, yana wa'azi a majimi'un su yana kuma fitar da aljanu. 40 Wani kuturu ya zo wurinsa. Yana rokonsa, ya durkusa. Ya ce masa, “in ka yarda kana iya warkar da ni. 41 Sai ya yi juyayi, Yesu ya mi ka hannun sa ya ta ba shi ya na ce masa “Na yarda. Ka sarkaka”. 42 Nan da nan kuturtar ta barshi, ya kuma sa mu tsarkakewa. 43 Yesu ya yi masa gargadi sosai, ya salame shi. 44 Ya ce masa “ka tabbata fa kada ka gayawa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, sai ka je ka yi hadaya domin tsarkakewa kamar yadda Musa ya umurta, domin shaida. 45 Amma da ya fita sai ya fara gaya wa kowa, ya baza maganar a ko'ina, har Yesu bai iya tafiya a sake a garin ba. Ya tafi ya tsaya a wuraren da ba kowa, mutane kuwa su ka zo wurinsa daga ko'ina.